fidelitybank

Wani babban al’amari zai faru a siyasar Kano da Najeriya – Kwankwaso

Date:

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran tafiyar darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya gargadi mabiyansa da su yi taka tsan-tsan tare da daina adawa a kan yin sulhu da abokin hamayyar sa na siyasa da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar.

PlatinumPost ta rawaito cewa tun bayan ziyarar ta’aziyyar da gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kai masa magoya bayan sa su ke ta tafo albarkacin bakin su a kai.

Ziyarar dai ta janyo cece-ku-ce kan cewa ’yan siyasar biyu da su ka rabu kai tsaye bayan zaben 2015, na gab da yin sulhu.

A cikin wani faifan bidiyo da a ke kyautata zaton Rahma TV ta dauka a lokacin da ta ke hira da Kwankwaso, abun ya sauya salo a siyasar Kano.

A cewarsa, jihar na karkata zuwa lokaci mafi muhimmanci a tarihin siyasarta, wanda ke bukatar zage-zage domin samun nasara, ya na mai kira ga mabiya Kwankwasiyya da su yi taka-tsan-tsan tare da daina adawa da sabbin matakan.

“Bari in yi amfani da wannan dama wajen gargadi mabiyanmu, wadanda ke cewa idan aka yi sulhu, za su fice daga jam’iyyar ko kuma kungiyar gaba daya.

”Ina gargadin su da su kiyaye kalaman su. Jihar mu ta na ganin sabon alfijir a tarihin siyasarta. Idan misali tafiyar siyasar mu mataki na 7 ne, to abin da zai biyo baya shi ne mataki na 6, zabe mai zuwa kuma shi ne mataki na 7. Wannan mataki na 7 shi ne mafi wahala da ke bukatar kwarewar siyasa da gogewa, domin cimma matsaya,” A cewar Kwankwaso.

Kwankwaso ya kara da cewa “Mu na gargadin mabiyan mu da su yi hattara kan wannan sabon babi a siyasar mu. Mutane ba sa yin furuci a kan abubuwan da ba su sa ni ba.

“Akwai wani babban al’amari da zai faru a siyasar Kano da ma Najeriya, domin haka ina gargadin mabiyan mu da su ba ta goyon baya, domin gudun yin nadama a lokacin da abin ya faru,” inji Kwankwaso.

Tsohon ministan ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su ba shi shawara kan duk wani abu da su ke ganin bai dace ba, ya na mai ba da tabbacin cewa za a kirga kuri’unsu a sabuwar tafiyar siyasar jihar.

sun newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp