Farfesa Charles Dokubo, tsohon shugaban shirin afuwa na shugaban kasa, PAP, ya mutu.
Dokubo ya mutu ne bayan gajeriyar jinya da ya yi a yammacin ranar Laraba.
An haifi tsohon shugaban afuwar ne a garin Abonnema, karamar hukumar Akuku Toru ta jihar Ribas a ranar 23 ga Maris 1952.
Dokubo ya yi karatun firamare da sakandare a garin Abonnema.
Ya yi matakinsa na ‘A’ a Kwalejin Fasaha ta Huddersfield da ke Yammacin Yorkshire. Daga 1978-1980, Dokubo ya samu gurbin shiga Jami’ar Teesside da ke Middlesbrough, inda ya yi kwas a fannin Tarihi da Siyasa na Zamani, sannan aka ba shi BA [Hons] a Jami’ar Bradford.
Ya kammala digirinsa na biyu a fannin nazarin zaman lafiya, kafin ya ci gaba da digirinsa na uku a fannin Yada Makamin Nukiliya da sarrafa shi.
A cikin 1985, an ba shi digiri na uku a Jami’ar Bradford.
Daga baya aka nada shi malami na wucin gadi a sashen kafin ya wuce Najeriya a shekarar 1993. In ji Daily Post.