fidelitybank

Tsohon gwamnan Kano zai jagoranci tawagar yaƙin neman zaɓen Osibanjo

Date:

Ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Yemi Osibanjo (OSO), ta naɗa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafizu Abubakar, a matsayin shugaban ƙungiyar da zai jagoranci gangamin yaƙin neman zaɓen 2023.

An dai tabbatar da naɗin nasa ne tare da wasu shugabannin tafiyar, yayin wani taron ƙungiyar da ya gudana a Kano ranar Asabar.

Farfesa Hafizu dai shi ne mataimakin gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje daga shekarar 2015 zuwa 2018.

Taron dai ya samu halartar kungiyoyin magoya bayan mataimakin shugaban ƙasar da suka fito daga sassa daban-daban na Najeriya.

Da yake jawabi yayin taron, Daraktan tsare-tsare na kungiyar, Bashir Suwaid, ya ce, akalla ƙungiyoyin da ke goyon bayan Osinbajo sama da 45 ne suka halarci taron.

Aminiya ta rawaito cewa, taron ya kuma zabi shugabanni daga dukkan shiyyoyin siyasa guda shida na ƙasar nan.

Sauran mukaman jagororin ƙungiyar sun hada da daraktan tsare-tsare da mai ba da shawara a bangaren shari’a da daraktan Kudi da na wayar da kan Jljama’a da na mulki da kuma na yaɗa labarai da dai sauransu.

legits news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram Takwas a jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kashe aƙalla...

Sauya sunan Kwaleji a Oyo ya fusata Dalibai

Ɗaliban kwalejin fasaha ta Ibadan sun gudanar da zanga-zanga...

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Dantata

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta'aziyya...

Trump ba shi da hankali ko tunani a kan harajin sa – Elon Musk

Tsohon mai ba shugaban Amurka Donald Trump shawara kan...

Dangote ya rage man fetur lita 840

Matatar man Dangote ta rage farashin litar man fetur...

Wa’adin da Najeriya ta bai wa Facebook na biyan tarar dala miliyan 290 ya cika

A ranar Litinin ne wa'adin da wata kotu ta...

Jami’an sa-kan Zamfara sun kashe Kacalla Ɗanbokolo ubangidan Turji

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin Najeriya...

PDP ta gudanar da taron ta na kasa

Shugabani da gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki...

An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

‘Yansanda sun kwace iko da sakatariyar PDP a Abuja

A yayin da ake ci gaba da takun-saka kan...

Iran ta na da ‘yancin yin Nukiliyar ta – Ravanchi

Iran ta dage kan hakkinta na ci gaba da...
X whatsapp