fidelitybank

Tsaro: ‘Yan ta’adda sun kashe mutane sama da 20 a Kaduna – Hukumomi

Date:

Gwamna jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya mika sakonta’azziya ga iyalan wadanda harin ‘yan ta’adda ya rutsa da su tare da yi musu addu’ar Allah ya jikan su,

Gwamnan ya kuma jajanta wa al’ummar da abin ya shafa, ya kuma umurci hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kaduna da ta gudanar da tantancewar cikin gaggawa a yankin domin bayar da agaji.

Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya sanar da hakan cewa, hukumomin tsaro na Soja da ‘yan sanda su ka kai wa Gwamnatin Jihar Kaduna rahoton cewa, an kashe mutane sama da 20 a harin da ‘yan ta’adda su ka kai wasu kauyukan karamar hukumar Giwa.

Za kuma a tantance sunayen wadanda a ka kashe da zarar an tabbatar da karin bayani daga gwamnatin jihar Kaduna. A halin yanzu, wanda jami’an tsaro sun ci gaba da sintiri a yankin baki daya,

A cewar rahoton, ‘yan ta’adda sun kai hari a kauyukan Kauran Fawa da Marke da Riheya da ke Idasu, a karamar hukumar Giwa, inda su ka kashe mutane sama da 20 har zuwa lokacin da a ka samu labarin.

daily post nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp