fidelitybank

Tsaro: ‘Yan Katsina ku mallaki Bindigar kan ku -Masari

Date:

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ja hankalin al’ummar jihar da su yi amfani da makamai domin tunkarar ‘yan bindiga da ke addabar su.

A cewar gwamnan yayin zantawa da manema labarai ya ce, jami’an tsaro kadai ba za su iya magance matsalar rashin tsaro a jihar ba.

Da ya ke jawabi yayin wani taron manema labarai a Katsina, Masari ya jaddada cewa yawan jami’an tsaro a jihar bai isa a shawo kan lamarin ba.

“A Musulunci ya halatta mutum ya kare kansa daga harin. Dole ne mutum ya tashi ya kare kansa, da iyalansa, da dukiyarsa. Idan ka mutu ka na ƙoƙarin kare kanka, za a ɗauke ka a matsayin shahidi. Abin mamaki ne yadda dan fashi zai mallaki bindiga alhali mutumin kirki da ke kokarin kare kansa da iyalansa ba shi da ita”.

Ya kuma yi nuni da cewa gwamnatin jihar za ta taimaka wa masu shirin mallakar makamai, domin kawo karshen matsalar ‘yan fashi da makami a jihar.

“Za mu goyi bayan wadanda su ka zo da shirin sayo makamai, saboda mazauna yankin na bukatar su kara kaimi ga kokarin hukumomin tsaro. Wadannan mutane (jami’an tsaro) ba su da yawan da za su kare jama’a.

“Lokacin da Shugaba Buhari ya zo, har ma ya yi kokarin kara yawan jami’an tsaron mu, amma abin bai wadatar ba. Ku lissafa kanku, ‘yan sanda nawa mu ke da su a kasar nan? Sojoji nawa mu ke da su?

“Ko da mu ka ce kowane dan sanda ya koma jiharsa, ba zai wadatar ba. Domin haka, idan mu ka ninke hannu mu ka yanke shawarar yin komai, za mu fi shan wahala”. Inji shi.

Masari ya ce,”‘Yan sanda za su yi rijistar duk bindigogin da mazauna garin su ka saya, domin tabbatar da an yi amfani da su yadda ya kamata. Katsina, kamar sauran jihohin Arewa maso Yamma, Zamfara, Kaduna, Sokoto, da Kebbi, sun sha fama da hare-haren kungiyoyin ‘yan ta’adda”. A cewar Masari

Rahotanni na nuni da cewa, Daruruwan mutane ne a ka kashe ko kuma a ka yi garkuwa da su a Katsina cikin wannan shekara tare da raba dubbai daga gidajen su.

 

naija hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp