fidelitybank

Tawagar jami’an tsaro sun mamaye gidan ajiya da gyaran hali na Jos

Date:

‘Yan ta’addan da suka kai hari gidan ajiya da gyaran hali na Medium Security da ke Jos a Jihar Filato a ranar Lahadin da ta gabata a yanzu haka an yi musu kawanya a cikin gidan.

Hakan ya fito ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Francis Enobore, ya fitar a daren Lahadi.

Ya kuma ce, “Mun fuskanci harin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa cibiyar, wanda su na da yawa da manyan makamai a hannun su. Duk da cewa sun samu shiga cikin gidan, amma duk da haka sun makale a ciki, inda nan take aka tara maza daga jami’an tsaro ‘yan uwa, domin su taimaka wa masu gadin da ke dauke da makamai, domin killace katangar da ma yankin baki daya”. Inji Francis.

Rahotanni ya nuna cewa, maharan sun shiga gidan ajiya da gyaran hali da misalin karfe Biyar da Ashirin na yamma, inda nan take suka nufi babbar kofar shiga gidan, inda su ka yi artabu da jami’an rundunar da ke dauke da makamai kafin su kutsa cikin farfajiyar gidan.

A na ci gaba da shawo kan lamarin, yayin da maharan su ka yi masayan harsashai da tawagar jami’an tsaro.

vanguard news nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp