A ranar Alhamis din nan Taiwan ta ba da kusan dala biliyan 19 don tsaronta a shekarar 2023, karin kusan kashi 14 cikin 100 daga jimillar kasafi da ake yi a yanzu.
Shawarar ta biyo bayan atisayen soji da China ta yi a tsibirin tun bayan ziyarar shugabar majalisar dokokin Amurka Nancy Pelosi.
Kuɗaɗen za su shafi sabbin jiragen yaƙi da shirye-shirye don haɓaka ƙarfin yaƙin teku da iska.
Kasafin kudin ya nufi majalisar dokoki, wadda za ta fara sabon zama a watan Satumba.
A watan Janairun da ya gabata ne Taiwan ta zartar da wani karin kudirin kashe kudi na kusan dala biliyan 9 don asusun tsaro na musamman na shekaru biyar, baya ga kasafin kudin shekara.
A shekarar 2022, kudaden da ake kashewa a fannin tsaro na kasar Sin ya karu da kashi 7.1 bisa dari zuwa yuan tiriliyan 1.45, wanda ya zarce na kasafin kudin shekarar 2021 na kashi 6.8 bisa dari.
Gwamnatin kasar Sin na ci gaba da yin Allah wadai da goyon bayan da kasashen waje ke ba wa Taiwan da ke da ‘yancin kai tun daga shekarar 1949.
A ranar 15 ga watan Agusta, mambobin majalisar dokokin Amurka sun gana da shugabar Taiwan Tsai Ing-wen da ‘yan majalisar dokoki.