fidelitybank

Taimakon da Dantata ya ke yi wa Al’umma tarihi ba zai manta da shi ba – Akpabio

Date:

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana alhininsa game da rasuwar fitaccen mai taimakon jama’a, Alhaji Aminu Dantata wanda ya rasu a ranar Juma’a.

Hakan na kunshe ne a cikin sakon ta’aziyyar mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Hon. Eseme Eyiboh, ranar Lahadi.

Akpabio ya bayyana marigayi Dantata a matsayin mutum mai kishin zuciya wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen taimakawa marasa galihu.

“Marigayi Aminu Dantata ya nuna kauna ga bil’adama ta yadda ya jajirce wajen ganin halin da talakawa da mabukata suke ciki, ayyukan taimakon sa ya kasance wanda ba za a manta da shi ba a tarihin kasarmu,” in ji Akpabio.

Ya kara da cewa ya san Dantata a matsayin mutum mai hazaka kuma mai kyauta wanda ya yi arzikinsa ta hanyar kwazo da sana’a.

Ya kara da cewa irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar Kano da Arewacin Najeriya da ma kasa baki daya na da dimbin yawa.

Shugaban majalisar dattawan ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Dantata, jama’a da gwamnatin jihar Kano, da ‘yan kasuwar Najeriya.

Ya bayyana marigayi dan kasuwan a matsayin ginshiki, wanda ya cancancta, kuma mutumin da ba za a iya mantawa da shi ba a Najeriya.

“A gaskiya Marigayi Dantata cibiya ce ta kan sa, ya cancanci a yi koyi da shi kuma ya dawwama,” in ji shi.

“A madadin iyalai na, da ‘yan mazaba, da Majalisar Dattawa, da kuma daukacin Majalisar Dokoki ta kasa, ina mika ta’aziyyata ga iyalan Dantata tare da addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba shi Aljannar Firdausi,” sanarwar ta karkare.

sspdf news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...

An gargadi Borno da Yobe da Jigawa su zama cikin shirin ambaliya

Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohin Borno, Jigawa da...

Kano na cikin jihohin da ba su yi katin zabe sosai ba – INEC

Bayanan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya...

Mun gano filin wasa na Sani Abacha ba shi da inganci – NPFL

Hukumar shirya gasar cin kofin kwararru ta kasa (NPFL),...

Jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna ya ya fadi

Jirgin ƙasa ɗauke da fasinjoji da ya taso daga...

Jami’in mu bai saci naira biliyan 6.5 ba – Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta karyata rahoton da ya zargi...
X whatsapp