Tawagar Super Eagles ta Najeriya wadda ta lashe kofin Afirka sau uku, ta rike matsayi iri daya a matsayin na baya bayan nan da hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fitar a safiyar Alhamis.
Super Eagles, wadanda ba su taka leda ba a watan Agusta na ci gaba da zama a matsayi na 31.
Haka kuma bangaren Jose Peseiro ya ci gaba da rike matsayi na hudu a Afirka.
Kungiyar Terangha Lions ta Senegal ce ta zama ta daya a nahiyar inda Atlas Lions ta Morocco da Carthage Eagles ta Tunisia a matsayi na biyu da na uku.
Babu wasu canje-canje a cikin 10 na farko a duniya yayin da Brazil, Belgium, Argentina, Faransa, Ingila, Spain, Italiya, Netherlands, Portugal, da Denmark suka ci gaba da kasancewa a matsayinsu.
A ranar Talata 27 ga watan Satumba ne Super Eagles za su fafata da Desert Foxes na Algeria a wasan sada zumunci a filin wasa na Miloud Hadefi, Oran.