Sanatan Kano ta kudu a majalisar dattawa, Malam Ibrahim Shekarau ya kai ziyarar ta’aziyya ga tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa rasuwar kanin sa.
Malam Ibrahim Shekarau ya kai masa ziyarar ne a gidan Kwankwaso na Miller Road da ke kwaryar birnin Kano.
A yayin ziyarar ta’aziyyar Shekarau ya samu tarba ta musamman daga wajen masoya bayan Kwankwasiyya a gidan na Miller Road.
sohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamdio ya kai makanciyar irin wannan ziyarar, a yayin da gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, shi ma ya kai ziyarar ta’aziyyar.