fidelitybank

Saudiyya ta fara shiri na 2 a kan muradan shekarar 2030

Date:

Mai kula da Masallatan Harami guda biyu, Sarki Salman ya bayyana cewa, an fara shirin kashi na biyu na muradan shekarar 2030 na Masarautar wanda ya kara kaimi ga nasarori da gyare-gyare da a ke ci gaba da yi.

Da ya ke kaddamar da ayyukan shekara ta biyu na zama na takwas na Majalisar Shoura a yammacin Larabar, Sarkin ya bayyana cewa manufar ta na da manufar tabbatar da ci gaban kasar nan da samar da makoma mai kyau ga al’ummarta ta hanyar samar da ingantaccen tsarin tattalin arziki mai ma’ana daban-daban wanda zai iya yin tasiri da sauye-sauyen duniya.

Yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman ya halarci taron bude taron majalisar, wanda ya bayyana manyan alfanun da ke tattare da manyan ayyukan da suka hada da samar da guraben ayyukan yi ga Saudiyya.

Ya kuma ce, “Mun albarkaci kaddamar da ayyuka da dama da Yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman ya yi tare da hangen nesa na gaba wanda ke goyon bayan dokokin Masarautar da kuma dorewarta, wadata, kirkire-kirkire, da jagoranci na kasuwanci. Waɗannan suna kawo ɗimbin guraben ayyukan yi da kuma babbar riba ga babban abin cikin gida na (GDP)”. Inji shi.

A yayin da ya ke bayyana manufofin masarautar cikin gida da waje, Sarkin ya ja hankali kan matsayin kasar Saudiyya a duniya bisa matsayinta ta na Larabawa da Musulunci, da kuma rawar da take takawa a fagen siyasar kasa da kasa, da kuma kudurin da ta dauka na kiyaye alkawuran da a ka dauka na tabbatar da tsaro da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali da wadata.

spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za mu kammala titin jirgi na Kaduna zuwa Kano a 2026 – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya, ta ce za a kammala aikin titin...

Adadin kudaden da Liverpool ta kashe wajen daukar ‘yan wasa

Liverpool ta kashe fam miliyan 265 wajen ɗauko ƴanƙwallon...

Sunderland ta ɗauko ƴanƙwallo bakwai a kakar bana

Granit Xhaka ya zaman ɗan ƙwallo na bakwai da...

James Trafford ya sake komawa Man City daga Burnley

Mai tsaron ragar tawagar Ingila, mai shekara 21, James...

Luiz Diaz ya kammala komawa Bayern Munich daga Liverpool

Luis Diaz ya kammala komawa Bayern Munich daga Liverpool...

NNPCL ya musanta sayar da matatar mai ta Fatakwal

Babban kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya musanta...

Mun samu kuɗin gina titin jirgi daga Maiduguri zuwa Abia – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta ce, ta samu duka kuɗin gudanar...

Sanatocin Arewa sun yi tir da kisan Zamfara

Ƙungiyar sanatocin Arewa, ta yi Allah wadai da kisan...

Tattalin arzikin Najeriya zai kara bunkasa a shekarar nan – IMF

Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya sabunta...

Ma’aikatan jinya sun fara yajin aiki a Najeriya

Ƙungiyar ma'aikatan jinya da unguzomomi ta kasa, ta fara...

Birtaniya ta na tsantsanr goyon bayam Hamas ne kawai – Netanyahu

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce, matakin da Birntaniy...

Birtaniya ta gindaya wa Isra’ila sharuɗa

Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya shimfiɗa wa Isra'ila wasu...
X whatsapp