Kungiyar rajin kare tattalin arzikin kasa (ESG) ta yi kira ga al’ummomin da suke hako mai a yankin Neja-Delta da su tallafa wa sojoji, domin magance satar danyen mai a yankunan su.
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar da sakatarenta, Okoro Anselem da Baba Usman suka fitar, sun koka da cewa kalubalen muhalli a jihar Rivers ya na faruwa ne sakamakon ayyukan satar danyen mai.
Kungiyar ta yi kira ga shugabanni da masu ruwa da tsaki da al’ummomin da ke da arzikin man fetur, ta ce, baya ga dimbin asarar tattalin arzikin da kasar ke fama da shi, satar danyen mai kuma ya na lalata muhalli.