Kungiyar al’adun kabilar Igbo ta Apex, Ohanaeze Ndigbo, ta zargi hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, da mayar da kanta a matsayin wani shiri na musgunawa mutanen Kudu-maso-Gabas a zaben shugaban kasa na 2023.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo Youth Council Worldwide, OYC, Mazi Okwu Nnabuike ya fitar ranar Talata.
Okwu, wanda ya yabawa tsohon gwamnan Imo, Sanata Rochas Okorocha kan shiga takarar shugaban kasa, ya ce, ya zama ruwan dare hukumar EFCC ta bi mutanen yankin Kudu maso Gabas da zarar sun nuna sha’awarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa.
A ranar Litinin ne hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta shigar da kara a gaban kotu kan tuhume-tuhume 17 a kan Okorocha, bisa zargin wawure kimanin Naira biliyan 2.9 a matsayin gwamna.
Da take mayar da martani, kungiyar ta OYC ta shawarci hukumar EFCC da kada ta koma cikin irin lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, inda ake amfani da hukumar wajen tsoratar da duk ‘yan siyasar adawa.