Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya karbi bakwancin tawagar kungiyar, Dattawan Arewa ta (Coalition of Northern Groups) a kan mika ta’aziyar rasuwar Alhaji Bashir Usman Tofa.
Shugaban kungiyar ya bayyana haka ne ta bakin jagorancin, Alhaji Ango Abdullahi a fadarsa.
Ya ce,”Ba za su taba manta irin gudunmawa da dabi’un marigayin, Alhaji Bashir Usman Tofa, saboda ya bayar da gudunmawa so sai a kasar nan wajen samun ci gaban ta”. Inji Ango.
A nasa jawabin mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya mika godiyar sa ga wannan ziyarar ta’aziyar da kungiyar Dattawan Arewa ta (Coalition of Northern Nigeria) ta kawo fadar sa a jihar Kano.