Wani jrigin dakon kaya daga Jihar Legas a kudancin Najeriya da ke kan hanyarsa ta zuwa Kano a arewaci ya sake yin hatsari a Jihar Kaduna.
Shugaban ma’aikatan hukumar sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC) ya faɗa wa BBC Hausa cewa, ‘yan bindiga ne suka lalata wani ɓangare na layin dogon, abin da ya sa jirgin ya kauce daga titinsa.
Hatsarin ya jawo mutuwar direban jirgin wanda rahotanni suka bayyana sunansa da Bala Kawu.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a Ƙaramar Hukumar Igabi, kusa da sansanin sojoji na Jaji. Wasu hotuna da aka yaɗa a shafukan zumunta sun nuna yadda jirgin ya kife a gefen titinsa.
Kazalika, hatsarin ya afku kwana uku bayan harin da ‘yan bindigar suka kai kan jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Abuja, wanda ya yi sanadiyyar kisan mutum takwas da jikkata kusan 40.