fidelitybank

Sai Akpabio da Wike da sauran jami’ai sun halarci asibitin Abuja don sanin halin dake ciki – Likitoci

Date:

Likitocin Abuja waɗanda suke yajin aiki sun ƙalubalanci Ministan Abuja Nyesome Wike da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio su riƙa amfani da asibitocin gwamnati da ke babban birnin tarayya, Abuja domin sanin halin da marasa lafiya suke shiga.

“Idan mun shirya gyara ɓangaren kiwon lafiya a ƙasar nan, ina tunanin ya kamata a tilasta wa jami’an gwamnati amfani da asibitocin gwamnati,” kamar yadda shugaban ƙungiyar likitocin Abuja, George Ebong ya bayyana a tattaunawarsa da tashar Channels a ranar Laraba.

“Zan so in fara ganin ministan yana zuwa asibitin Wuse, zan so ganin shugaban majalisar dattawa yana zuwa asibitin Maitama, sannan mu ga shugaban majalisar wakilai yana zuwa asibitin Nyanya. Idan aka fara haka ne za a iya gyara ɓangaren kiwon lafiya, amma matuƙar ba sa amfani da su, maganar gaskiya ba za a iya gyara su.”

Tun da farko, likitocin na Abuja sun faɗa yajin aiki ne a ranar Laraba saboda wasu haƙƙoƙinsu bayan wa’adin mako uku da suka bayar ya ƙare.

legit new

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp