Mataimaka shugabannin jam’iyya PDP na ƙasa sun ce shugabancin riƙon ƙwarya na Umar Damagun ba zai ƙare ba har sai zuwa watan Disamban bana.
Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar, Timothy Osadolor ne ya bayyana haka a madadin sauran mataimakan shugabannin jam’iyyar, inda ya ƙara da cewa dukkan masu adawa da shugaban su yi haƙuri har zuwa lokacin da wa’adinsa zai ƙare a watan Disamba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Sun ce suna kira ga waɗanda suke adawa da shugabancin Damagun su daina ɓata sunan jam’iyyar, su ba shi dama ya yi aikinsa.
A game da muƙamin sakataren jam’iyyar, sun ce maganar na kotu, don haka suka ce Sanata Anyanwu ne suka ganin ya fi kamata ya riƙe muƙamin har zuwa lokacin da kotu za ta warware matsalar, sannan suka yi kira ga shugabannin jam’iyyar su haɗa hannu domin tabbatar da mulki ya dawo hannun PDP a zaɓen 2027.