Wata babbar kotun tarayya a Kano, ta yankewa wani dan kasar Kamaru, Wamba Jean-Gaston mai shekaru 41, hukuncin daurin shekaru biyar a gidan gyaran hali, bisa samunsa da laifin safarar wasu matasa mata uku da maza hudu daga kasar Kamaru zuwa Najeriya daga nan kuma ya wuce da su Turai.
Matan uku da abin ya shafa su ne: Belinga Ovanda mai shekaru 19 da Koussene Agnes, mai shekaru 21 da Meye Uwono mai shekaru 27 yayin da mazan su ne Thomas Ange, mai shekaru 21 da Ovanda Rodrigue, mai shekaru 21 da Boris Kouass, mai shekaru 20 tare da Yannick Poudjom, mai shekaru 18.
Mai shari’a Abdullahi Muhammed-Liman ya yankewa Jean-Gaston hukunci, bayan ya amsa laifuka biyu da ake tuhumarsa da shi.
Liman ya bayyana damuwarsa kan tasirin da mai laifin ke da shi ga rashin tsaro a yankin baki daya da ya shafi kasashe da dama.
Tun da farko, Lauyan hukumar hana safarar mutane ta kasa (NAPTIP), Mista Abdullahi Babale, ya shaidawa kotu cewa, an kama wanda ake tuhuma a Kano ranar 10 ga watan Disamba, 2021.
Babale ya ce, an kama dan Kamarun ne tare da mutanen bakwai da aka kashe a kan hanyarsu ta zuwa kasar Aljeriya.
Ya ce, mai laifin ya na sarrafa takardun shiga ba bisa ka’ida ba ga wadanda aka yi safarar su zuwa kasashen Algeria da Turai ta Najeriya da Jamhuriyar Nijar, ba tare da takardar izinin zama ko biza ba.
Lauyan ya ce, laifin ya sabawa sashe na 26 (1) na dokar tilastawa mutane fataucin mutane, 2015.