fidelitybank

Rundunar Sojin Ƙasa ta yaye sojoji mayaƙa 525

Date:

A yau Litinin ne Rundunar Sojin Ƙasa ta yaye sojoji mayaƙa 525 waɗanda za a kakkai su zuwa bataliyoyi daban-daban a faɗin ƙasar nan.
Da ya ke jawabi a yayin bikin yaye sojojin a sansanin horon sojoji da ke Kachia a Jihar Kaduna, Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa na Ƙasa, Laftanal Janar Faruk Yahya ya baiyana cewa Nijeriya ta samu kayan yaƙi domin samun nasarar yaƙi da rashin tsaro.
Ya kuma yi kira ga  dakarun da su jajirce su ga sun kare kayan yaƙin da ga ɓatagari.
Ya ce an tsara horon sojin ne karo na 80 tare da ɗaukar sojoji masu jini a jika domin koya musu ƙwarewa domin a samu rundunoni masu ƙarfi.
Shugaban ya ƙara da cewa horon Ya sakawa sabbin sojin ƙaimi, ƙwarewa da kuma laƙantar yaƙi da a ke buƙata wajen aiwatar da aikin soja daban-daban da a ke bukata wajen kare Nijeriya.
Ya yi kira ga sojin da a ka yaye da su dage su yi amfani da horon da su ka samu a duk inda su ka tsinci kan su a filin daga domin kare ƙasa Nijeriya.

today nation

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...

Rasha tarnaki ce a wajen Tarayyar Turai – Jamus

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya shaidawa BBC cewa...

Amurka ba ta goyon bayan Isra’ila a harin Syria – Trump

Amurka ta ce ba ta goyon bayan hare-haren da...

Tinubu zai zo Kano ta’aziyyar Dantata

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai kai ziyara Kano yau...

Tarayyar Turai tamince da ƙaƙaba wa Rasha sabbin takunkumai

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta amince da ƙaƙaba wa Rasha...

Gwamnan Filato ya zargi Jami’ai da kin kama ‘yan bindiga

Gwamnatin jihar Filato ta zargi jami'an sojojin ƙasar da...

Za a yi wa Buhari addu’a a Abuja

Gwamnatin Tarayya za ta jagoranci gudanar da taron addu'o'i...

Buhari ya ban umarni na kula da Talakawan Najeriya – Peter Obi

Jagorar jam'iyyar LP a Najeriya, Peter Obi ya ce,...

Sojojin hadin gwiwa sun hallaka ‘yan Boko Haram a tafkin Chadi

Rundunar hadin gwiwa mai yaƙi da Boko Haram a...

Na yi rashin aboki na gari kuma Najeriya ta rasa mutumin kirki – Tinubu

Shugaban Kasa, Bola Tinubu, na ci gaba da alhinin...
X whatsapp