A yau Litinin ne Rundunar Sojin Ƙasa ta yaye sojoji mayaƙa 525 waɗanda za a kakkai su zuwa bataliyoyi daban-daban a faɗin ƙasar nan.
Da ya ke jawabi a yayin bikin yaye sojojin a sansanin horon sojoji da ke Kachia a Jihar Kaduna, Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa na Ƙasa, Laftanal Janar Faruk Yahya ya baiyana cewa Nijeriya ta samu kayan yaƙi domin samun nasarar yaƙi da rashin tsaro.
Ya kuma yi kira ga dakarun da su jajirce su ga sun kare kayan yaƙin da ga ɓatagari.
Ya ce an tsara horon sojin ne karo na 80 tare da ɗaukar sojoji masu jini a jika domin koya musu ƙwarewa domin a samu rundunoni masu ƙarfi.
Shugaban ya ƙara da cewa horon Ya sakawa sabbin sojin ƙaimi, ƙwarewa da kuma laƙantar yaƙi da a ke buƙata wajen aiwatar da aikin soja daban-daban da a ke bukata wajen kare Nijeriya.
Ya yi kira ga sojin da a ka yaye da su dage su yi amfani da horon da su ka samu a duk inda su ka tsinci kan su a filin daga domin kare ƙasa Nijeriya.