Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Ganduje, ya jaddada kudirinsa na ci gaba da bunkasa jihar duk kuwa da yunkurin da wasu ‘yan siyasa ke yi na kawo tsaiko a jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a gidan gwamnatin jihar Kano, a ranar Lahadin da ta gabata, tare da halartar dukkan bangarorin masu ruwa da tsaki.
Ya ce, “Ya na da matukar muhimmanci kowa ya san cewa hazakarmu ta siyasa da gogewar siyasarmu ba za su bari rikicin kananan jam’iyya ya karkatar da hankalinmu wajen kara bunkasa jiharmu ta Kano ba. Abin da ke faruwa wani bangare ne na al’adar dimokuradiyya,” inji Ganduje yayin da ya ke mayar da martani kan rikicin jam’iyyar APC na Kano.
Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da ‘yan majalisar wakilai 20, kakakin majalisar dokokin jihar Kano, da ‘yan majalisar dokokin jihar 28, da shugabannin kananan hukumomi 44, dukkan shugabannin jam’iyyar APC mai mulki daga mazabar 484 da kananan hukumomi 44 da kuma shugabannin jam’iyyar na jihar da dattawan jihar da dai sauran su, wadanda su ka halarci taron, sun kada kuri’ar amincewa da gwamnan.
A cewar sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan jihar, Anwar Abba, wanda PlatinumPost ta samu a ranar Lahadin da ta gabata, Ganduje yayin da ya ke tunatar da masu ruwa da tsaki a kan tsarin da a ka bi a taron gundumomi da na kananan hukumomi na jam’iyyar, ta ce dukkanin hanyoyin sun bi ka’idoji.
A kan shirin da wasu ‘yan siyasa ke yi na kawo ruguza sha’anin mulki a jihar, Ganduje ya ce shi ba sabon salo ba ne a irin wannan salon siyasar.