fidelitybank

Orji Uzo Kalu mutum ne mai son ci gaban kasa da kishin al’umma – Ahamd Lawan

Date:

Shugaban majalisar dattawa ta kasa, Sanata Ahmad Lawan, ya yabawa Kibiyan Kebbi kuma bulaliyar majalisa, Sanata Orji Uzo Kalu, bisa irin gudunmawar da ya ke baiwa majalisa dama kasa baki daya.

Sanatan Ahmad Lawan ya bayyana Kibiyan Kebbi, Orji Uzo Kalu a matsayin mutum mai kishin al’umma, sakamakon gudunmawar da ya ke baiwa ‘yan kasa.

Sanarwar mai kunshe da sa hanun mai taimaka masa a harkokin Arewa, Aminu Shehu Uba Sharada, a yayin da Orji Uzo Kalu ke mika sakon ta’aziyar sa ga daukacin al’ummar muslmai da jihar Sokoto na kona mutane da ‘yan ta’adda su ka yi.

Ya ce,”Kibiyan Kebbi, mutum ne dan yankin Kudu maso Gabas, amma ya fi karfi a Arewacin kasar nan, ni na rasa yadda zan bayyana shi, saboda gudunmawar da ya ke bayarwa wajen hada kan ‘yan kasa da gina al’umma.

Ya kuma ce”Amma gaskiya wannan ya nuna cewa mutum ne mai kishin Najeriya, na zauna daki daya da shi a jami’ar Maiduguri a shekarar 1980, a matsayin dalibai, na san ba zai baiwa ‘yan Najeriya kunya ba, wajen hada kan ‘yan kasa, mutum ne kuma mai yi wa kasa addu’a na samun zaman lafiya a zama wuri guda, kuma dama mu addu’ar mu kenan wajen zama Najeriya dunkulalliya, mu aikin mu shugabanni shi ne, mu wakilai ne na hada kan kasa da al’umma, kuma kamar yadda mu ke ‘yan majalisu a yanzu shi ne Najeriyar ce a gaban mu, mun yarda cewa Najeriya daya ce, kuma za mu sa Najeriya a gaba, saboda al’umma mu ke yi wa aiki, kuma dukannin mu mun fito daga mazabun mu”. Inji Sanata Ahmad Lawan.

 

www.najnew

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

‘Yan Arewa su dakata da neman mulki har zuwa 2031 – Sakataren Gwamnati

Sakataren gwamnatin tarayya, SGF, George Akume, ya yi kira...

Matatar Dangote ta janye ƙarar da ta shigar kamfanin NNPCL a kotu

Matatar man Dangote ta janye ƙarar da ta shigar...

Ba mu baiwa Obi shawara ya janye daga takara ba – Kungiyar Inyamurai

Kungiyar koli ta al’adun kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo Worldwide,...

Dole ne APC ta bar mana kujerar mataimakin shugaban kasa – ANPP

Tsagin tsohuwar jam'iyyar All Nigeria Peoples Party wato ANPP...

Gwamna ya nada Sarkin Gusau

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya amince da naɗin...

‘Yan Bindiga sun yi ikirarin kashe Daliban koyon aikin lauya a Benuwai

Ƴanbindiga da suka yi garkuwa da ɗaliban makarantar samun...

Tinubu ya gwangwaje tawagar Super Falcons da ruwan daloli da gidaje a Abuja

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bai wa ƴan wasan...

Super Falcons ta sauka a Abuja tare da yin zagayen nuna kofi

Tawagar Super Falcons ta Najeriya sun isa Abuja bayan...

Za a fuskanci katsewar wutar lantarki a Legas tsawon kwana 25

Masu amfani da wutar lantarki a jihar Legas na...

‘Yan Najeriya ku daina bayar da bayan katin dan kasar ku – NIMC

Hukumar Kula da shaidar ɗan ƙasa (NIMC), ta bayyana...

Likitoci a Legas sun fara yajin aiki saboda rage musu albashi

Ƙungiyar likitoci ta Legas (Medical Guild), wacce ke ƙarƙashin...

Yan Bindiga sun yi wa Mutane 38 yankan Rago a Zamfara

Ƴanbindiga sun kashe wasu mutum 38 ta hanyar yi...
X whatsapp