fidelitybank

Caccakar Gwamna: Sarkin Adamawa ya tsige Mukaddas Adamawa

Date:

Mai martaba sarkin Adamawa, Lamidon Adamawa, Muhammadu Barkindo, ya tsige guda daga cikin mai rike da sarautar gargajiya a jihar, bisa sukar, Gwamna jihar Ahmadu Fintiri kan bayar da kyautar mota ga sarakunan gargajiya a jihar.

Majalisar Masarautar Adamawa ta ce yanzu Umar Mustapha bai cancanci rike sarautar gargajiya ta ‘Mukaddas Adamawa’ ba. Sakamakon sukar da ya yi.

Mustapha wanda tsohon dan takarar gwamna ne a karkashin jam’iyyar APC, a wata sanarwa da ya fitar ya caccaki gwamna Ahmadu Fintiri kan kyaututtukan da ya yi.

“Abin da bai dace ba ne a kashe Naira miliyan 200 domin samun motoci ga sarakunan gargajiya yayin da ‘yan fansho ke mutuwa saboda yunwa,” inji Tsohon Mukaddas Adamawa Umar.

Sanarwar ta biyo bayan sanarwar da gwamnatin jihar ta yi wa sarakunan gargajiya.

Bayan sanarwar, Sarkin, Barkindo, a wata sanarwa ta hannun sakataren masarautar, Khalil Kawu, ya ce an tsige Mustapha daga mukamin sa.

 

 

naija news today legits

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Najeriya na cece-kuce dangane da rasuwar Muhammadu Buhari

Mutuwar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta bar cece-kuce ga...

Da Ɗumi-Ɗumi: Kashim Shettima zai rako gawar Muhammadu Buhari zuwa Najeriya

Tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya rasu. Ya rasu ne...

Ina Tinubu ya ke ya ɓata ba bayani – ADC

Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC, ta soki Shugaba,...

Koriya ta Arewa za ta ba Rasha ƙarin sojoji domin yaƙin Ukraine

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya yi...

Jam’iyyar ADC alheri ce ga siyasar Najeriya – Femi Gbajabiamila

Shugaban ma'aikata na fadar gwamnatin Najeriya, Femi Gbajabiamila ya...

Tinubu na yunkurin tauye hakkin ma’aikata – Atiku

Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a Najeriya, Atiku Abubakar, ya...

Trump ya lafta wa ƙasashen Tarayyar Turai da Mexico harajin kashi 30

Shugaban Amurka Donald Trump ya lafta wa ƙasashen ƙungiyar...

INEC ta ce za ta buɗe shafin intanet domin rajistar sababbin jam’iyyu

Huhukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC, ta ce nan...

EFCC na neman Rabi’u Auwalu Tijjani ruwa a jallo a Kano

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin...

An gano musabbabin hatsarin jirgin saman Indiya

Masu bincike sun bayyana sakamako na farko-farko game da...

Amurka ta haramta wa shugaban kasar Cuba shiga kasar

Amurka a karon farko ta ƙaƙaba takunkumi kan shugaban...

An kashe mutum 6,800 tare da sace 5,402 a 2025 Najeriya – Rahoto

Alƙaluma na nuna cewa an kashe mutum dubu shida...
X whatsapp