fidelitybank

Omicron: Matakin Birtaniya zalinci ne da horo – Lai Muhammed

Date:

Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga gwamnatin Birtaniya da ta janye matakin hana shiga ƙasar daga Najeriya saboda nau’in korona ta Omicron.

Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ne ya yi kiran yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin,

Ya ce”Babu hikima a wannan matakin, duk da cewa kwamatin yaƙi da korona na shugaban ƙasa zai ɗauki matakin da ya dace, ni a matsayina na mai magana da yawun gwamnati ina kallon matakin a matsayin zalinci da horo”.

Ya ƙara da cewa matakin na Birtaniya ba a ɗauke shi ta fuskar kimiyya ba, sannan ya bayyana mamakinsa kan “ta yadda za a ɗauki matakin kan ƙasa (Najeriya) mai al’umma fiye da miliyan 200 kawai, saboda tsirarun mutanen da suka kamu da cutar”.inji Lai.

BBC ta rawaito cewa, Ofishin jakadancin Birtaniya a Najewriya ya dakatar da bayar da biza ga ‘yan Najeriyar sakamakon haramcin tafiyar da aka saka.

Shi ma kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na British Airways ya soke dukkanin tikitin shiga Birtaniya daga Najeriya, inda ya nemi fasinjojin su sauya lokaci ko kuma wurin tafiya.

fg spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mu na aiki tuƙuru wajen daƙile ayyukan ta’adda a Najeriya – Christopher Musa

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatarwa...

Mayaƙan ISWAP sun harbe Manoma 23 a Borno

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar mayaƙan ISWAP ta kashe...

Real Madrid ta ɗauki ɗan wasan baya daga Bournemouth

Real Madrid ta sanar da sayen ɗan wasan baya...

Gwamnatin Kano ta haramta yin bikin Ƙauyawa da gidajen biki

Hukumar tace fina-finai a jihar Kano ta sanar da...

An kashe ƴan Boko Haram biyar a Borno

Dakarun sojin Najeriya haɗe da wasu maharba sun daƙile...

Farashin Shinkafa zai cigaba da sauka – BUA

Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya alƙawarta...

An kashe mutane 10 a wani sabon rikici da ya ɓarke a Filato

Aƙalla mutabe 10 ne aka kashe tare da sace...

Duk da sauƙin da aka samu har yanzu Abuja na fuskantar hauhawar farashi

Duk da cewa hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS, ta...

Hauhawar farashi ya ragu da kaso 23.71 a Najeriya – NBS

An samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya daga...

Fiye da mutane 100 Makiyaya aka kashe a Jos

An ruwaito cewa an kashe wani makiyayi guda da...

Tinubu ka kori shugaban JAMB – Sowore

Dan siyasa mai fafutuka, Omoyele Sowore, ya yi kira...

Majalisa ta yi watsi da ƙudirin karɓa-karɓa

Majalisar wakilai ta yi watsi da wani ƙudirin doka...
X whatsapp