fidelitybank

Mutuwar Dr. Ahmad babban rashi ne ga al’ummar musulmai – Ganduje

Date:

Gwamna jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana rasuwar Dr Ahmad Muhammad Ibrahim Bamba, fitaccen malamai a cibiyar Darul Hadith da ke Kano, a matsayin babban rashi na jiga-jigan masu samar da zaman lafiya da kuma tarin ilimin Hadisi.

Dr. Ganduje ya sanar da hakan ne ta hannun babban sakataren yada labaran sa, Abba Anwar, wanda ya rabawa manema labarai.

Mutuwarsa ba karamin rashi a a ka yi wa jihar ba. Ya kara da cewa, marigayi malamin ya kasance hazikin malami, mai zurfin hazaka da asali, a cikin karantarwarsa na fadin manzon Allah Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

“Ya kasance mai karfafa zaman lafiya tare a cikin lumana, wanda tsarin koyarwarsa ya kasance da nufin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin dukkanin bangarori da ma sauran su. Wannan babban rashi ne da ke tattare da bakin ciki da rashin maye gurbinsa,” in ji gwamnan.

Gwamna Ganduje ya bukaci malaman addinin Musulunci da su yi kokari tare da yin koyi da kyawawan halaye na marigayi Sheikh. Ya na mai jaddada cewa, “Ya kafa ginshikin yadda a ke yin Da’awa kuma ya bi abin da ya ke wa’azi. Mutum mai daraja ta kowane hali.”

Da ya ke ci gaba da cewa, “A madadin gwamnati da al’ummar jihar Kano, ina mika ta’aziyyarmu ga iyalan Sheikh Dr Ahmad Muhammad Ibrahim, ba wai iyalansa ba, Kano ko Nijeriya baki daya, duk al’ummar duniya baki daya sun yi asarar wani abu mai wuyar gaske.”

Ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta masa dukkan kurakurensa, ya kuma saka masa da alherinsa da Jannatul Fiddaus.

news today in nigeria 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp