fidelitybank

Mutane 19 sun mutu yayin da 26 suka jikkata a Kano – FRSC

Date:

A kalla mutane 19 ne suka mutu yayin da wasu 26 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a Bagauda kusa da harabar makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya da ke kan hanyar Kano zuwa Zaria.

Kwamandan hukumar kare aukuwar hadura ta kasa FRSC a jihar Kano, Zubairu Mato, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Alhamis a Kano.

Ya ce, hadarin ya rutsa da motocin Hiace guda biyu na kasuwanci mai lamba KBT 152 XA da NSR 275 ZX.

“Mun samu kira da misalin karfe 7:30 na safiyar ranar 6 ga Janairu, 2022. Da samun labarin, mun yi gaggawar aika jami’an mu da motar mu zuwa wurin da lamarin ya faru, domin ceto wadanda abin ya shafa da karfe 7:40 na safe,” in ji Mato.

Kwamandan sashin ya ce, hatsarin ya auku ne, sakamakon gudun wuce kima, lamarin da ya kai ga karo da juna inda motocin biyu suka yi taho mu gama da wuta. Hatsarin ya shafi jimillar fasinjoji 45 a cikin motocin bas guda biyu, daga cikinsu maza 14 da mata hudu sai wani yaro namiji daya da suka rasa rayukansu yayin da wasu 26 suka samu munanan raunuka,” inji shi.

Mato ya ce,”An kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Kura, domin yi musu magani, yayin da a ka mika gawarwakin sauran ga ‘yan uwansu da ke ofishin ‘yan sanda na Bebeji”. A cewar Mato.

Kwamandan sashen ya shawarci masu ababen hawa da su guji yin gudu, kima a kan ababen hawan su.

 

vanguard news nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp