Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutane 11 a Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf da ke Jihar Kaduna.
Ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ce tabbatar da hakan cewa, an kai harin ne a Kurmin Masara da ke Zangon Kataf ɗin da safiyar Lahadi.
Bayan mutanen da aka kashe, akwai waɗanda aka tabbatar da cewa sun samu raunuka haka kuma an ƙona sama da gidaje 30.
Gwamnatin Kadunan ta ce, sojojin sama da suka yi ƙoƙarin kai ɗauki an yi musu kwanton ɓauna a hanyarsu ta zuwa wurin da lamarin ya faru.
Sai dai sojojin sun samu galaba a kan waɗanda suka yi musu kwanton ɓauna tare da dakarun Operation Safe Haven domin isa Kurmin Masara.