fidelitybank

Mun karbi shari’u 292 a shekarar da ta gabata a Kano – Labaran Kabo

Date:

Majalisar taimakawa a bangaren shari’a ta kasa reshen jihar Kano, ta ce ta karbi korafe-korafen shari’u na mutane 292 a bara.

Ko’odinetan majalisar, Labaran Kabo ne ya bayyana haka a zantawarsa da manema labarai  a ranar Lahadi a Kano.

Ya ce, daga cikin shari’o’in 292, akwai 232 na kan laifuka ne yayin da 60 kuma na fararen hula ne.

ya kuma ce, “Laifukan sun hada da kisan kai, fyade, fashi da makami, karya amana, da kuma sata, yayin da shari’ar farar hula ta shafi aure, gado, rikicin filaye da karbo bashi,” inji shi.

Kabo ya kara da cewa, a tsawon lokacin da majalisar ta kammala tantance kararraki 69 yayin da 223 ke ci gaba da shari’a a kotuna.

“Hukumar mu ita ce tabbatar da daidaito da adalci ga dukkan ‘yan Najeriya ta hanyar ba da tallafin shari’a kyauta da taimako ta hanyar da ke nuna ainihin manufofin tsarin mulki da manufofin gwamnati na samun adalci,” in ji shi.

A cewarsa, majalisar ta na ba da  ‘yanci ga kowa. Ya kuma shawarci wadanda ba za su iya biyan kudi wajen daukan lauya da su tuntube su.

tribune news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp