fidelitybank

Bankin kasa CBN ya rage kudin da bankuna ke cajar mutane

Date:

Babban Bankin Kasa (CBN) ya ba da umarnin a rage kuɗin da bankunan ke caza yayin cire kuɗi ta ATM da kuma tura kuɗin ta intanet tsakanin bankuna.

Matakin na ƙunshe ne cikin wata sanarawa da Chibuzor Efobi, shugaban sashen kula da tsare-tsaren kuɗi da dokoki, ya fitar ya na mai umartar bankuna da cibiyoyin kudi da su sauya tsarin.

CBN ya ce, an ɗauki matakin ne saboda a tabattar bankunan na bin sabbin tsarin da kasuwanci ke tattare da shi.

Sauyin ya shafi kudin Naira 65 da ake cazar mutum idan ya ciri kuɗi ta ATM na bankin da ba nasa ba sau uku cikin wata ɗaya, inda aka mayar da shi Naira 35.

Haka nan kuma an rage cajin aika kudi ta intanet tsakanin bankuna daga N300 zuwa N50 a matsayin mafi yawan adadin da za a caji mutum.

Akwai tsarin bin diddigin ayyukan bankunan domin tabbatar da cewa an daƙile yawan cazar mutane ba tare da amincewarsu ba.

vanguard (nigeria)

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mu na aiki tuƙuru wajen daƙile ayyukan ta’adda a Najeriya – Christopher Musa

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatarwa...

Mayaƙan ISWAP sun harbe Manoma 23 a Borno

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar mayaƙan ISWAP ta kashe...

Real Madrid ta ɗauki ɗan wasan baya daga Bournemouth

Real Madrid ta sanar da sayen ɗan wasan baya...

Gwamnatin Kano ta haramta yin bikin Ƙauyawa da gidajen biki

Hukumar tace fina-finai a jihar Kano ta sanar da...

An kashe ƴan Boko Haram biyar a Borno

Dakarun sojin Najeriya haɗe da wasu maharba sun daƙile...

Farashin Shinkafa zai cigaba da sauka – BUA

Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya alƙawarta...

An kashe mutane 10 a wani sabon rikici da ya ɓarke a Filato

Aƙalla mutabe 10 ne aka kashe tare da sace...

Duk da sauƙin da aka samu har yanzu Abuja na fuskantar hauhawar farashi

Duk da cewa hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS, ta...

Hauhawar farashi ya ragu da kaso 23.71 a Najeriya – NBS

An samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya daga...

Fiye da mutane 100 Makiyaya aka kashe a Jos

An ruwaito cewa an kashe wani makiyayi guda da...

Tinubu ka kori shugaban JAMB – Sowore

Dan siyasa mai fafutuka, Omoyele Sowore, ya yi kira...

Majalisa ta yi watsi da ƙudirin karɓa-karɓa

Majalisar wakilai ta yi watsi da wani ƙudirin doka...
X whatsapp