fidelitybank

Mun fara shirin tsawaita rayuwar al’ummar Nijeriya — NSCC

Date:

 

Wata sabuwar hukuma mai suna Cibiyar Kula da Tsofaffi ta Ƙasa, NSCC, ta ci alwashin ɓullo da shirye-shirye da za su tsawaita rayuwar al’ummar Nijeriya, wanda a turance a ke kira da ‘life expectancy’.

Darakta Janar ta cibiyar, Emem Omokaro ce ta baiyana hakan a wata ganawa da Kanfanin Daillancin Labarai, NAN a jiya Lahadi a Abuja.

Omokaro ta ƙara da cewa cibiyar za ta bunƙasa rayuwar tsufa har ta zama abar sha’awa a Nijeriya.

A cewar Omokaro a shekarar 2015 da 2018, Nijeriya tana ta can ƙasa a jerin ƙasashe masu tsayin rayuwa na duniya sabo da a lokacin babu wasu ajiyayyun bayanai da zai sanya ta kasance a saman jerin sunayen.

“A na yin jerin sunayen ne ta hanyar duba da irin kula da kuma jin daɗi da tsofaffi ke samu a ƙasa, da kuma wasu matakai da su ke yin nuni da hakan, misali, wa’adin tsawon rayuwa na tsofaffin mutane da dai sauran matakai.

“A Nijeriya, mutane su ke kaiwa shekaru 60, in ma sun kai, mutane nawa ne ke samun cikakkiyar lafiya da rayuwa bayan shekara 60 ɗin. Nawa ne a cikinsu su ke samun inshorar rayuwa da kuma kuɗaɗen kashewa?

“Amma yanzu, da zuwan NSCC, wa’adin tsawon al’ummar Nijeriya zai ƙaru sabo da a yanzu muna da Doka ta Shekaru a Nijeriya. Mun tanadi wani kundin tsari na tsawon shekaru 10 sannan kuma dokar da ta kafa NSCC za ta taimaka gudanar da shirin,” in ji Omokaro.

Ta ƙara da cewa” kwanan nan tsawon wa’adin shekarun ƴan Nijeriya zai ƙaru sabo da shirye-shiryen da mu ka tanada za su sanya ƴan Nijeriya su samu tsawon rai, za kuma a ƙarawa tsofaffi kulawa ta musamman,” in ji ta.

nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp