fidelitybank

Mu na da hujja a kan rufe sansanin ‘yan gudun hijira – Zulum

Date:

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce, an rufe dukannin sansanonin ƴan gudun hijira da ke jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a saƙon murnar sabuwar shekara da ya fitar, inda ya ce, matakin da a ka ɗauka na rufe dukannin sansanonin an ɗauke shi ne, domin ƙara inganta rayuwar jama’a.

A makon da ya gabata, ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama sun roƙi hukumomi da su janye wannan kudirin na su, sakamakon gwamnati ba ta da tabbaci na kula da haƙƙoƙin ƴan gudun hijira.

Ƙungiyoyin sun yi gargaɗin cewa, yunƙurin da a ke yi na mayar da ƴan gudun hijira muhallansu zai sa rayukan sama da iyalai 10,000 cikin hatsari, sakamakon irin hare-haren da ƴan Boko Haram da ƴan ISWAP ke ci gaba da kai wa da kuma zargin cin zarafi da sojoji ke yi.

Sai dai Gwamna Zulum ya dage kan cewa, sansanonin sun soma zama wurare da ake aikata munanan abubuwa iri-iri, ciki har da karuwanci da sayar da miyagun ƙwayoyi da kuma daba a wasu lokutan.

BBC ta rawaito cewa, sama da ƴan gudun hijira miliyan 1.8 ne a ka mayar garuruwan su domin ci gaba da gudanar da rayuwarsu.

latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp