fidelitybank

Mu kungiyoyi ne na duniya da dangogin mu dake tallafa mana – IPOB

Date:

Haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) a ranar Talata ta ce magoya bayanta na gida da na waje sun kasance tushen daukar nauyin su.

Sakatariyar yada labaran kungiyar, Emma Powerful ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce, “A karo na goma sha uku, babu wani mutum daya da zai iya daukar nauyin kungiyar IPOB. Mu ƙungiyoyi ne na duniya kuma miliyoyin dangin mu a gida da waje sun kasance tushen tallafin mu.

“Ba mu taba boye wannan gaskiyar ba, saboda mu ba kungiya ce ta sirri ko ta’addanci ba. IPOB ta na da tushe mai kyau kuma ba ma bukatar wani Okorocha ko Uche Nwosu ko Hope Uzodinma ko wani dan siyasa kan lamarin ya dauki nauyin mu. Ba mu da mu’amala da gurbatattun ‘yan siyasa da mutanen da ke da shakku kan tushen arzikin su.” inji IPOB.

In za a iya tunawa cewa, IPOB kungiya ce mai fafutukar neman ballewa a Najeriya, babban burinta shi ne dawo da kasar Biafra mai cin gashin kanta a tsohon yankin Gabashin Najeriya, wanda ya kunshi yankunan Kudu maso Gabas da Kudu-maso-Kudu a yau; ta hanyar zaben raba gardama na ‘yancin kai.

An kafa kungiyar ne a shekarar 2012 a hannun Nnamdi Kanu, dan gwagwarmayar siyasar Najeriya dan kasar Birtaniya wanda ya yi fice wajen fafutukar neman ‘yancin kasar Biafra.

punch newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp