fidelitybank

Mata su rungumi hadin kai gabannin 2023 – Aisha Buhari

Date:

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta gargadi ‘yan uwanta mata da su rungumi hadin kai gabanin babban zabe na 2023.

Naija News ta rawaito cewa, Uwargidan shugaban kasar ta ba da shawarar ne a ranar Litinin yayin da ta ke karbar bakwancin mataimakin shugaban Laberiya, Jewel Howard-Taylor.

Mataimakiyar ta ziyarci Najeriya ne, domin halartar babban taron mata na jam’iyyar APC na kasa.

Da ta ke jawabi a wajen taron, Aisha Buhari ta ji dadin ‘yan jam’iyyar APC da ke kan iyakokin kasar da su yi amfani da sabbin dabaru, domin tabbatar da cewa mata da yawa sun shiga cikin yanke shawara.

Ta kuma jaddada cewa, hadin kan matan zai taimaka musu wajen yin tasiri mai karfi a harkokin zabe.

Uwargidan shugaban Najeriyar ta kuma bukaci masu ruwa da tsaki da su tallafa wa jinsin mata, domin cimma bukatar su na kara shiga harkokin siyasa. Ta ce: “Akwai bukatar a karfafa mata gwiwa, domin su kara shiga harkokin siyasa, kuma kasar na bukatar shigar mu. Ya zama dole mu sanya ido kan yadda za mu yi aiki tare, domin hada kan mata a yakin neman zabe mai zuwa gabanin zaben 2023.”

Aisha ta kara da cewa “Na gamsu cewa tarihinki a matsayinki na tsohuwar uwargidan shugaban kasar Laberiya, kuma kwararriya kan harkokin siyasa zai kara kima a taron”. In ji Aisha

Da take yabawa kasancewar Howard-Taylor a wurin taron, Misis Buhari ta ce, kalaman za su karawa mata kwarin gwiwar halartar taron.

 

taraba news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp