fidelitybank

Jagoran kungiyar IPOB zai sake gurfana a gaban kotu

Date:

A yau ne ake sa ran sake gurfanar da jagoran ƴan awaren Biafra, Nnamdi Kanu da sabbin tuhume-tuhume 15 na ta’addanci a gaban kotu.

Sabbin tuhume-tuhumen wadanda aka gabatar da su ranar Litinin sun zo ne ƙasa da sa’o’i 24 kafin a sake shiga kotu a ci gaba da shari’ar da ake yi masa.

Nnamdi Kanu zai sake gurfana a kotun Abuja, bisa tuhumar cin amanar ƙasa da ta’addanci, da kafa haramtacciyar ƙungiya, laifukan da hukuncinsu hukuncin kisa ne idan sun tabbata.

Wannan ne karo na biyu da gwamnati ke yin kwaskwarima kan tuhume-tuhumen da ake yi wa jagoran na ƙungiyar IPOB.

An fara kama Kanu ne a 2015, bisa tuhume-tuhimen ta’addanci da jagorantar haramtaciyyar ƙungiya da wallafa munanan kalamai, da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba da kuma shigar da miyagun kaya ƙasar ta Najeriya.

Nnamdi Kanu wanda ya ke da fasfo na ƙasar Birtaniya, kuma ya daɗe a ƙasar, sannan an mai da shi Najeriya, to amma har yanzu gwamnati ba ta bayyana daga wata ƙasa aka tissa ƙeyarsa ba.

daily post newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farashin Shinkafa zai cigaba da sauka – BUA

Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya alƙawarta...

An kashe mutane 10 a wani sabon rikici da ya ɓarke a Filato

Aƙalla mutabe 10 ne aka kashe tare da sace...

Duk da sauƙin da aka samu har yanzu Abuja na fuskantar hauhawar farashi

Duk da cewa hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS, ta...

Hauhawar farashi ya ragu da kaso 23.71 a Najeriya – NBS

An samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya daga...

Fiye da mutane 100 Makiyaya aka kashe a Jos

An ruwaito cewa an kashe wani makiyayi guda da...

Tinubu ka kori shugaban JAMB – Sowore

Dan siyasa mai fafutuka, Omoyele Sowore, ya yi kira...

Majalisa ta yi watsi da ƙudirin karɓa-karɓa

Majalisar wakilai ta yi watsi da wani ƙudirin doka...

Labarin mu na kaiwa Ƴan Bindiga abinci ƙarya ne – Ƴansanda

Rundunar ƴansandan Najeriya ta musanta rahotannin da ake yaɗawa...

Ba za mu yarda mu mutu a cikin PDP ba shi yasa muka koma APC – Sanatoci

Sanatocin Najeriya uku da suka fito daga jihar Kebbi,...

Sojoji sun tarwatsa wajen da ake hakar man fetur ba bisa ka’ida ba a Rivers

Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya, NNS, Pathfinder, ta tarwatsa...

Dan Tinubu Seyi da sauran ‘yan Siyasa sun fara neman kujerar gwamnan Legas

Siyasar Legas na kara ruruwa na neman maye gurbin...

Mayakan IS sun yi wa Sojojin Najeriya barna a kwana biyu

Mayaƙan IS sun ƙara kai wa sojojin Najeriya hari,...
X whatsapp