Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya ce, man fetur tare da sauran albarkatun fadin kasar nan dukkan su na ‘yan Najeriya ne, ba wain a iya wani yankin ba.
Obasanjo ya bayyana haka ne a wani martani da ya mayar wa fitaccen dattijon nan na yankin Naija Delta, Cif Edwin Clark, wanda ya zargi Obasanjo da nuna halin ko-in-kula game da illolin da hakar mai a yankin na su ya haddasa.
Wasu rahotanni sun nuna cewa Clark, a cikin wata wasika da ya rubuta, yana zargin tsohon shugaban kasar ya nuna kiyayya ga masu fafutukar mallakar albarkatun kasar da a ka samu a yankunan su.
Sai dai a martanin da ya mayar, Obasanjo ya ce, a iya saninsa albarkatun kasar nan da a ka hako a Najeriya mallakin dukkanin ‘yan kasar nan ne ba na mutanen yankunan da a ka same su ba. A cewar BBC.
Ya kara da cewa”Ba zai yiwu a samu kasashe biyu a cikin kasa daya ba, ya na mai cewa, a iya fahimtarsa Cif Clark ya na magana ne a kan samar da wata kasa a cikin Najeriya idan har ya na so a baiwa Naija Delta damar mallakar albarkatun kasar da a ka samu a yankin”.
A cewarsa, “Kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya yarda cewa zinaren da a ka samu a Zamfara, ko “zinaren da a ka samu a Ilesha da ke Jihar Osun, da kuma ma’adinin lead da ke Jihar Ebonyi” shi ne kuma ya bayyana cewa fetur din da a ka samu a Naija Delta duka na ‘yan kasar ne”.
Obasanjo ya kara da cewar,”Dukkan mutanen da su ka kulla yarjejeniyar sayen danyen man fetur sun yi ne da Najeriya a matsayin kasa ba da yankin Naija Delta ba, inna mai jaddada cewa, Najeriya dunkulalliyar kasa ce da babu wanda ya isa ya raba ta, ciki har da raba albarkatun da ke cikinta”.
A cewarsa: “Idan akwai wata barazanar tsaro a kowanne bangare na Najeriya a yau, ciki har da yankin Naija Delta, sojojin Najeriya ne tare da tallafin wasu jami’an tsaro, a matakin gwamnatin tarayya, za su yi raddi kan hakan”. Inji Obasanjo.
Masu fafutuka a yankin Naija Delta sun dade suna kokarin ganin sun mallaki fetur din da ake hakowa a yankinsu, inda a wasu lokutan lamarin yakan kai ga kashe-kashe da satar ma’aikatan man fetur.