fidelitybank

Majalisar Dattijai da Wakilai: An bankado badakalar Naira biliyan 8.5

Date:

Ofishin binciken kudi na tarayya ya bankado badakalar Naira biliyan 8.5 a zaurukan majalisar dokoki ta tarayya.

Rahoton binciken kudin ya gano yadda shugabancin zaurukan biyu suka kashe Naira biliyan Uku a majalisar dattawa da wasu biliyan 5.5 a majalisar wakilai a shekarar 2019 ba tare da shaidar kashe kudaden ba.

Mai binciken kudi na tarayya, Aghughu Adolphus, a rahoton sa, ya bankado yadda majalisar dattawa da majalisar wakilai da hukumar kula da harkokin majalisar dokoki ta kasa suka kashe kudaden ba bisa ka’ida ba.

Rahoton da ya gabatar wa Akawun Majalisar a watan Agusta ya ce,  an kashe kudaden ne a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2018 ba tare da cike takardun da suka dace ko rasitin kayan da a ka saya ba.

A shekarar da ta gabata ne kwamitin kudaden gwamnati na majalisar ya kaddamar da bincike kan hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya daga 2015 zuwa 2018.

A watan Yunin bana ne kwamitin da rahoton binciken wata shidan da ya gudanar a kan hukumomin.

Da ya ke bayani kan lamarin, shugaban cibiyar bin diddigi da tabbatar da gaskiya a harkokin majalisa (CISLAC), Auwal Musa Rafsanjani, ya ce wannan abin takaici ne kamar yadda Aminiya ta rawaito.

Sai dai a martaninsa, Akawun Majalisar Tarayya, Austen Adesoro, ya ce abubuwan da ake batu sun shafi shekarar 2019 kuma tuni a ka shawo kansu.

legitnews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp