fidelitybank

Mahukuntan Sudan su tabbatar da mulkin farar hula – Amurka

Date:

Kasar Amurka ta bukaci shugabannin kasar Sudan da su tabbatar da mulkin farar hula tare da kawo karshen tashin hankalin da a ke yi wa masu zanga-zanga bayan, Abdalla Hamdok ya yi murabus daga mukaminsa na firaminista, lamarin da ya jefa r’yan kasar zaman zulumi.

A cikin wata sanarwa da ofishin kula da harkokin Afrika na ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar a shafin Twitter ya sanar cewa, “Bayan murabus din da Hamdok ya yi na radin kansa, ya kamata shugabannin Sudan su ajiye bambance-bambance a gefe, su kuma samar da daidaito, tare da tabbatar da ci gaba da mulkin farar hula,” in ji ofishin.

Hamdok, wanda masanin tattalin arziki ne, kuma tsohon jami’in Majalisar Dinkin Duniya da kasashen duniya ke mutuntawa, ya taba zama Firayim Minista a karkashin yarjejeniyar raba madafun iko da sojoji da farar hula da su ka biyo bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir a shekarar 2019.

Sojoji sun rusa gwamnatinsa a wani juyin mulki a watan Oktoba, amma bayan wata guda ya dawo karkashin yarjejeniyar da ta dora masa alhakin kafa gwamnati kafin zabe a 2023.

thisdaynews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp