fidelitybank

Rikicin Ukraine: Amurka za ta mayar da martani kan Rasha – Biden

Date:

Fadar White House ta ce shugaban Amurka Joe Biden, ya shaidawa shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskiy cewa, Amurka da kawayenta za su mayar da martani mai tsauri idan Rasha ta kara mamaye Ukraine.

Wannan kiran dai ya zo ne kwanaki kadan bayan da Biden ya yi wata tattaunawa ta biyu a cikin wata guda da shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, a cikin tashe-tashen hankula a kan iyakar Rasha da Ukraine, inda Rasha ta tara dakaru kusan 100,000.

“Shugaba Biden ya bayyana karara cewa, Amurka da kawayenta za su mayar da martani mai tsauri idan Rasha ta kara mamaye Ukraine,” in ji kakakin fadar White House Jen Psaki a wata sanarwa da ya fitar kamar yadda kamfanin dilancin labarai na Reuters.

Biden da Zelenskiy sun tattauna shirye-shiryen gudanar da jerin tarurrukan diflomasiyya masu zuwa a nan gaba, domin magance rikicin, a cewar fadar White House.

Zelenskiy ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter cewa, sun tattauna matakan hadin gwiwa kan wanzar da zaman lafiya a Turai da kuma hana ci gaba da ruruwa.

Wakilai daga Amurka da Rasha na shirin yin wata tattaunawa a tsakanin ranakun 9 zuwa 10 ga watan Janairu a birnin Geneva, sai kuma tattaunawar majalisar Rasha da NATO da kuma taron kungiyar tsaro da hadin gwiwa a Turai.

Biden ya ce ya shaida wa Putin cewa ya na da muhimmanci Rashawa su dauki matakai domin sassauta rikicin kafin wadannan tarurrukan.

@nnn.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Dangote ya rage farashin litar mai zuwa ₦820

Kamfanin matatar man Dangote ya rage farashin litar mai...

Dubai ta sake tsaurara matakan bai wa ‘yan Najeriya biza

HaÉ—aÉ—É—iyar Daular Larabawa, UAE ta sake sanya wasu dokoki...

‘Yan Bindigar Katsina ‘yan asalin jihar mu ne – Gwamna

Gwamnan Katsina Umaru Dikko Radda ya ce galibin 'yan...

Zan yi wa ADC aiki ina cikin jam’iyyar PDP – Sule Lamido

Jigo a babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya...

Buhari da Tinubu kan su a hade ya ke – Garba Shehu

Mai magana da yawun tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari...

Ganduje ya kama aiki a hukumar kula da filayen jirgin sama

Tsohon shugaban jam'iyyar APC mai mulki, Abdullahi Ganduje, ya...

JAMB ta amince da maki 150 mafi Æ™anÆ™anta don samun gurbin karatu a jami’o’i

Hukumar shirya jarrabawar shiga Jami'o'i ta Najeriya (JAMB) ta...

ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya, ASUU da dakatar yajin...

Masu haÉ—akar ADC na É“aÉ“atu ne saboda rashin gwamnati – Radda

Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda ya yi...

Ba ruwan Biri da gada a makamin Nukiliya – Shettima

Mataimakin shugaba Najeriya Kashim Shettima ya ce ƙasar za...

An kashe Mutane 70 a jihar Filato

Rahotonni daga jihar Filato na cewa Æ´anbindiga sun kai...

Ambaliya ta kashe mutane 100 a Amurka

Hukumomi a jihar Tesxas da ke Amurka sun bayyana...
X whatsapp