fidelitybank

League 1: Monaco ta kori Kovac tsohon kocin Munich

Date:

Kungiyar Monaco ta kasar Faransa ta sallami tsohon kocin Bayern Munich da Croatia, Niko Kovac.

Monaco ta nada Kovac mai shekaru 50 a watan Yulin 2020 domin maye gurbin dan kasar Spain Robert Moreno, wanda a ka kora bayan watanni bakwai kacal.

Monaco ta ce an sanar da Kovac game da hukuncin ranar Alhamis kuma a hukumance ta sanar da shi ranar Asabar.

Kocin kungiyar, Stephane Nado ne zai jagoranci kungiyar a wasan da za su kara da kungiyar Quevilly-Rouen a gasar cin kofin Faransa ranar Lahadi.

Kovac, wanda ya lashe gasar Bundesliga na Jamus da kofi biyu da Bayern a kakar wasa ta 2018-19, ya karbi ragamar horar da Monaco sau 74, kuma ya bar ta na shida a kan teburi da tazarar maki 17 tsakaninta da Paris St-Germain.

An rawaito Philippe Clement na Club Bruges shi ne wanda a ka fi so ya maye gurbin Kovac.

nhgsfp

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp