Newcastle ta tuntubi Arsenal da ta ba ta aron dan wasan kasar Gabon, Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 32, a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa ta bana, da nufin biyan fan miliyan 20 a bazara.
Newcastle, ta kuma ce za ta biya sama da £50m a kan dan wasan Benfica kuma dan kasar Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 22.
Jami’an Newcastle na fatan kammala cinikin dan wasan bayan Atletico Madrid da Ingila Kieran Trippier, mai shekara 31, nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.