fidelitybank

Kwastam ta kama Bindugu cikin kwantaina

Date:

Jami’an Hukumar Kwastam ta Najeriya sun kama wani kwantaina makare da bindigogi da aka yi fasakwaurinsu daga kasar waje.

Sanarwar da jami;in hulda da jama’a na hukumar shiyar Tin Can Island, Uche Ejesieme, ya sanar ga manema labarai cewa, sun kama mutumin ne wanda ya yi musu karya da sunan talabijin din bango wato Plasma ya shigo da su zuwa Najeriya.

Uche Ejesieme, ya ce, “Jami’an hukumar mu sun yi nasarar kama wata kwantaina da ke dauke da makamai, tuni kuma a ka killace ta sai an kammala bincike a kanta, domin tabbatar da iya adadin makaman da kuma sauran muhimman bayanai. Yanzu haka za mu je mu yi wa kwantainar filla-filla domin mu tabbatar da iya yawan makaman da ta dauko da mutanen da ke da hannu wajen yin fasakwaurin makaman da sauran bayanan da suka dace da za mu fitar a nan gaba.”

Uche ya kuma ce,”Tun da farko sai da jami’an hukumar mu ka sa ayar tambaya a kan kayan da ke cikin sundukin, lura da yadda masu kula da kayan ke ta karba-karba wajen yin fitonsu. Bayan an kammala bincike za mu sanar da cikakken bayani game da miyagun makaman da mu ka kama ta hannun shelkwatar hukumar da ke Abuja”.

Hukumar ta kuma yi alkawarin yin dukkan mai yiwuwa wajen ganin an kamo duk mutanen da suke da hannu a shigo da makaman, da nufin magance matsalar fasakwaurin makamai zuwa Najeriya. Inji Aminiya.

latest nigeria newstoday

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp