Wani mummunan hadarin mota da ya afku a kan titin Aminu Kano, da ke unguwar Goron Dutse, yayin da wani direban mota kirar Toyota Corolla ke yunkurin wuce wata mota kirar Peugeout 406.
Wadanda suka gane wa idonsu yadda hadarin ya afku, sun ce, hadarin ya faru ne sakamakon gudun wuce-sa’a da direban motar yake yi.
Afkuwar hadarin ke da wuya, sai tawagar Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kano, Dr. Kabiru Ibrahim Getso ta iso wurin. Nan take Kwamishinan, wanda yake kuma kwararren likita ne, ya nuna tausayawarsa, ya ba da gudumawar gaggawa, kuma ya umarci a dauki wadanda suka ji rauni kafin a kai su zuwa asibiti.
Cikin Sanarwar da jami’in hurda da jama’a na Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kano Sunusi A. Kofar Naisa ya rabawa manema labarai ya ce, Dr. Getso ya yi addu’ar samun sauki ga wandanda suka ji raunuka. Sannan ya gargadi direbobi da su guji tukin ganganci da gudun-wuce-sa’a.