fidelitybank

NDLEA ta kama fasfo din kasashen waje a cikin buhun Gari

Date:

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta kama fasfo din kasa da kasa guda 22 na kasashe shida daban-daban da aka boye a cikin buhun Gari da dai sauran kayayyakin abinci.

Jami’an tsaro sun kama su ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammed International na Ikeja dake jihar Legas, a harabar tashar SAHCO da ke filin jirgin a lokacin da suke aikin binciken kayan da suka saba yi.

Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin, ya ce tara daga cikin fasfo din uku ne kowannen su na Birtaniya da Faransa da Portugal da na Najeriya 8 da Ghana 4 da kuma na Kamaru 1.

Ya kuma ce a filin jirgin, jami’an sun kwato fakiti 12 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 4.95 da aka boye a cikin kwalin Golden Morn da aka shirya domin fitar da su ta cikin rumbun ajiyar kayayyaki na SAHCO.

A halin da ake ciki, Babafemi ya bayyana cewa, a jihar Filato, tawagar jami’an NDLEA a ranar Juma’a 28 ga watan Janairu, sun kama wasu mutane biyu da ake zargi ciki akwai Emeka Ezenwa mai shekaru 37 da Julius Akingbe mai shekaru 45 da haihuwa, bisa laifin mallakar gram 126.5 na sinadarin methamphetamine da aka boye a cikin na’urar DVD da ta taho daga Legas.

assu today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Tinubu ya miʙa saʙon ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...

Trump ya yaudari Amurkawa da Iran – Aragachi

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya bayyana cewa...

Sai an hukunta Mutanen da suka kashe Ę“an ɗaurin aure – Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi Alla-wadai da...

An fara binciken fashewar wani abu da ya kashe mutane 5 da jikkata da dama a Kano

Wani abin fashewa da ake tunanin bom ne ya...

An samu fashewar wani abu a kamfanin ʓan Chana a Kano

An samu fashewar wani abu a Kamfanin ʘarfe na...

Ma’aikacin kamfani ya kashe abokin aikinsa a Kano

Rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta ya...

Kotu ta ɗaure Matashin da yake tare titi a Kano da sunan barʙwanci

Kotun majistire da ke unguwar Nomansland a Kano, karkashin...

Bayan kashe Soja yanzu haka an kama ʓan Daba 398 a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna, ta sanar da kama...

Shettima zai san makomarsa bayan taron APC na ʙasa – Fadar Shugaban ʘasa

Fadar shugaban ʙasa ta bayyana cewa, sai bayan babban...

Kotu ta ɗaure Matashin da ya shiga ɗakin kwanan ʊalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ʙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ʙaryata...
X whatsapp