Koriya ta Arewa ta kara harba makamai masu linzami biyu, a cikin kasa da makwani biyu.
Lamarin ya jawo suka da kuma neman tattaunawa daga gwamnatin Amurka da ta kara kakaba wasu sabbin takunkumi kan harba makaman da Koriya ta Arewa ta yi.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa, wannan dai shi ne harba makami mai linzami na uku da Koriya ta Arewa ta yi a cikin kasa da makwanni biyu kenan.
Sai dai kasar Amurka ta yi Allah wadai da harba na baya-bayan nan, ta na mai cewa hakan barazana ce ga makwabtan Koriya ta Arewa da kuma kasashen duniya.
A cikin wata sanarwa ta imel mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sake yin kira da a tattauna.
“