fidelitybank

Kano ta fi kowace jiha yawan almajiari – Ganduje

Date:

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ,ya bayyana cewa jihar ce ta fi kowace jiha yawan Almajirai a kasar nan.

Da ya ke magana da manema labarai yayin ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa dake Abuja, gwamnan ya koka da cewa, yawancin Almajirai ba ’yan asalin jihar ba ne.

Ya ce,“Eh, mu ne mafi yawan yaran Almajirai a Najeriya. Amma bari in gaya muku, mun dauki kididdiga. Yawancin wadannan Almajirai ba ’yan asalin jihar Kano ba ne, kuma a matsayinsu na ’yan Najeriya, suna da ’yancin zama a duk inda suke a kasar nan.

“Amma abin da ke da muhimmanci, mun bullo da ilimin firamare da sakandare kyauta, kuma wajibi a jihar Kano. Mun gina makarantun Islamiyya da dama. Mun gyara tsarin karatun Almajiri. Haka kuma, mun fara mayar da Almajiri zuwa jihohinsu, wasu har zuwa Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Kamaru”.

“Domin haka kokarin da mu ke yi kenan. Amma kamar yadda na fada muku, matukar ba a samu hadin kai ba, musamman a tsakanin gwamnonin jihohin Arewa, inda aka yi dokar hana Almajiri daga wannan jiha zuwa wata jiha, Kano za ta ci gaba da fama da wannan matsalar.” In ji Ganduje.

vanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp