fidelitybank

Kano Pillars za ta dawo Kano wasa nan ba da jimawa ba – Lakwaya

Date:

Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta gina wa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars sansanin ‘yan wasa da sakatariya.

Kwamishinan matasa da cigaban harkokin wasannnin na jahar Kano, Kwamrade Kabir Ado Lakwaya ya tabbatar da hakan yayin bude babban taron masu ruwa da tsaki na hukumar wasan kwallon kafa ta jahar Kano na shekara ta 2021.

Ya ce”Za a gina sansanin ‘yan wasan ne da za su rinka kasance wuri guda da sakatariyar a tsohuwar tashar manyan motoci da ke kan titin New road a unguwar sabon gari.

Ya kuma ce”Shirye-shirye sun yi nisa, domin samar da kayayyakin wasanni ga kungiyoyi sama da dubu biyu a Kano”.

Lakwaya ya kara da cewa,”Gwamnatin jihar ta na yin kokarin ganin an samar da sabuwar ciyawa a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata, domin ganin nan ba dadewa ba kungiyar Kano Pillars ta dawo gida Kano da buga wasannin ta na gasar Premier ta kasa, maimakon yadda ta ke buga wasannin ta a jihar Kaduna”.

Lakwaya ya kuma yabawa hukumar wasanni kwallon kafa ta jihar Kano karkashin jagorancin, Dr. Sharif Rabi’u Inuwa Ahalan, bisa yadda ta ke kokari wajen samar da ci gaban harkokin wasannnin kwallon kafa a jihar da kuma hade kan masu ruwa da tsaki a kan wasanni kwallon kafa wuri guda.

A nasa bangaren shugaban hukumar kwallon kafa ta jihar Kano, Dr. Sharif Rabi’u Inuwa Ahalan, ya godewa gwamnatin jihar, bisa kulawar da ta ke baiwa harkokin wasannni.

Ya kuma ce taron ya tattauna kan yadda za a gudanar da zabuka a matakan kwamitocin kanan hukumomi.

latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp