Tsohon dan wasan kwallon kafa na Barcelona, Samuel Eto’o, ya zama sabon shugban hukumar ƙwallon ƙafa ta kasar Kamaru.
Tsohon tauraron ɗan wasan na Kamaru da ƙungiyoyin Inter Milan da Barcelona ya doke muƙaddashin shugaba Seidou Mbombo Njoya a zaɓen da a ka gudanar ranar Asabar.
An kaɗa ƙuri’un ne bayan kotun sasanta harkokin wasanni ta soke nasarar Mista Njoya a zaɓen 2018.