fidelitybank

Juyin Mulki Sojoji: A gaggauta gudanar da zabe a kasar Mali

Date:

Wani taro a kasar Mali da a ka dorawa alhakin ba da shawarar jadawalin gudanar da zabukan dimokuradiyya bayan juyin mulkin da sojoji su ka yi, ya bayyana cewa ya kamata a jinkirta zaben da aka shirya yi a watan Fabrairu tsakanin watanni shida zuwa shekaru biyar a wani bangare na batun tsaro.

Tun farko dai gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali ta amince da gudanar da zabe a watan Fabrairun shekarar 2022, watanni 18 bayan da bangaren soji karkashin jagorancin Kanar Assimi Goita ya hambarar da gwamnatin shugaba Boubacar Ibrahim Keita.

Amma bai samu ci gaba kadan ba, ya na zargin rashin tsari da tashin hankalin masu kishin Islama a Arewa da tsakiya.

Kungiyar ECOWAS wadda ita ce babbar kungiyar siyasa da tattalin arziki a yammacin Afirka, ta sanya takunkumi kan shugabannin da su ka yi juyin mulki a sakamakon haka, ta kuma yi alkawalin karawa idan har Mali ba ta samar da wani shiri na zaben watan Fabrairu nan da ranar 31 ga watan Disamba ba.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa, gwamnatin kasar ta ce za ta dauki shawarwarin taron sake fayyace kasa da kuma yanke shawara kan sabon jadawalin zabe a karshen watan Janairu.

Tsawaita mika mulki ga mulkin demokradiyya zai iya mayar da kasar Mali saniyar ware daga makwabtanta daga tsohuwar mulkin mallaka Faransa wadda ke da dubban sojoji a can wajen yaki da masu tada kayar baya masu alaka da al Qaeda da IS.

tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp