fidelitybank

Jigawa ta hana yin fim da wakokin soyayya da na siyasa a jihar

Date:

Hukumar tace fina-finai ta jJihar Jigawa ta ce masu shiryawa da daukar fim, ko rera wakoki na siyasa da na soyyaya ko na fim, da masu yi musu rawa da su dakatar da harkokinsu a jihar har sai sun yi rijista da hukumar.

Daraktan hukumar tace fina-finai ta jihar, Yusuf Magaji, ya shaida wa BBC cewa sun dauki matakin ne bayan daraktan fim din nan mai suna ‘Makaranta’ ya bayyana cewa a jihar ya dauki fim din.

Fim din ‘Makaranta’ ya nuna abubuwa da dama da É—umbin jama’a suke ganin ba su dace a yi fim a kansu ba, wadanda suka hada da madigo da batsa da makamatansu.

“Mun yi haka ne saboda mu tantance wadanda suke shigowa jihar. Akwai wani fim da aka shirya wai shi ‘Makaranta’ inda shi wanda ya shirya shi jihar Kano take nemansa ruwa a jallo. sai yake cewa ba a Kano ya shirya ba, a Jigawa ne. A gaskiya bai zo wurinmu ya nemi izinin shirya fim din ba,” a cewar Yusuf Magaji.

Ya kara da cewa daraktan ya yi furucin ne da zummar shafa wa Jigawa kashin-kaji, domin haka su ma daga yanzu ba za su bari a rinka yin abubuwan da suka keta dokoki da al’adun jiharsu ba.

Masu shirya fina-finai masu dogon zango sun bayyana amincewarsu da wadannan matakai da gwamnatocin jihohin Kano da Jigawa suka dauka, suna masu yaba wa matakan.

Lawan Ahmad, tauraron fim ne kuma mai shirya fim din dogon zango na Izzar So, kuma ya shaida mana cewa su dama sai sun mika fina-finansu an tantance kafin su sanya a YouTube.

“Mu dama can muna bayar da fina-finan mu a duba. Sai dai idan an samu tsaiko ko wata matsala saboda yanayin aiki shi ne za ka ga ba mu bayar ba. Amma maganar gaskiya yadda wasu suke amfani da YouTube wajen saka abubuwan da ba su dace ba, ya kamata a sanya musu ido,” in ji shi.

A cewarsa matakin da hukumar tace fina-finai ta dauka yana da amfani “saboda kare al’ada da addininmu.

legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp