fidelitybank

Janar Qasem: A gurfanar da Trump ko mu dauki fansa – Iran

Date:

Shugaban kasar Iran, Ibrahim Raisi ya lashi takobin daukar fansa a kan kisan da Amurka ta yi wa marigayi Janar Qasem Soleimani shekaru biyu da suka gabata, matukar ba a gurfanar da tsohon shugaban Amurka Donald Trump a gaban kotu ba.

Iran da kungiyoyin da ke kawance da ita a Iraki sun gudanar da bukukuwan girmama Soleimani, kwamandan dakarun Quds, reshen dakarun kare juyin juya hali na kasashen ketare.

An kashe Janar Qasem a Iraki a wani harin da jiragen yaki mara matuka suka kai ranar 3 ga Janairu, 2020, wanda shugaba Trump na lokacin ya ba da umarnin.

“Idan ba a gurfanar da Trump da (tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo a gaban kotu ba, to gaskiya kan laifin kisan Janar Soleimani za su dauki fansar shahadar mu,” in ji Raisi a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin a ranar Litinin.

A ranar Lahadin da ta gabata, Iran ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a cikin wata wasika da ya kama Amurka da Isra’ila, wadanda Tehran ta ce su ma suna da hannu a kisan, kamar yadda kafafen yada labaran Iran suka rawaito.

Kwanaki bayan kisan, Amurka ta shaidawa Majalisar Dinkin Duniya cewa kisan kare dangi ne, ta kuma sha alwashin daukar karin matakin “kamar yadda ya dace” a yankin Gabas ta Tsakiya, domin kare ma’aikatan Amurka da muradunta.

vanguard newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

INEC za ta fitar da sabbin ƙa’idojin duba sakamakon zaɓe

A shirye-shiryen da take yi gabanin babban zaɓen Najeriya...

Isra’ila ta amince da sharuÉ—É—an yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Isra'ila ta amince...

Buhari ba zai taÉ“a cin amanar Tinubu ba – Garba Shehu

Tsohon babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai...

Mutane 207 ne suka mutu a ambaliyar Neja – NSEMA

Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta...

Jiga-jigan jam’iyyar PDP za su sauya sheÆ™a don tunkarar APC a 2027

Wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP da suka hada da tsohon...

Za a Æ™addamar da jam’iyyar hammaya da za ta tunkari APC

Gamayyar jam'iyyun adawa a ranar Talata, ta amince da...

Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram Takwas a jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kashe aƙalla...

Sauya sunan Kwaleji a Oyo ya fusata Dalibai

ÆŠaliban kwalejin fasaha ta Ibadan sun gudanar da zanga-zanga...

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Dantata

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta'aziyya...

Trump ba shi da hankali ko tunani a kan harajin sa – Elon Musk

Tsohon mai ba shugaban Amurka Donald Trump shawara kan...

Dangote ya rage man fetur lita 840

Matatar man Dangote ta rage farashin litar man fetur...
X whatsapp